Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka

Biden zai tattauna da Zelensky na Ukraine ta wayar tarho kan Rasha

Shugaba Joe Biden na Amurka na shirin tattaunawa da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ta wayar tarho a yau lahadi, tattaunawar da za ta mayar da hankali kan alakar kasar da Rasha da kuma barazanar Vladimir Putin na Rasha ga mulkin shugaban.

Shugaba Joe Biden yayin zantawarsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho ranar 30 ga watan Disamban 2021.
Shugaba Joe Biden yayin zantawarsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho ranar 30 ga watan Disamban 2021. - WHITE HOUSE/AFP/File
Talla

Tattaunawar ta Biden da Zelensky na zuwa ne kwanaki kalilan bayan makamanciyarta da Putin na Rasha a ranar 30 ga watan Disamaban 2021 wadda ta mayar da hankali kan rikicin Moscow da Kiev bayan girke dakarun da Putin ya yi a iyakar kasar wadda ta sanya fargabar yiwuwar mamaya kamar yadda ya yiwa yankin Crimea a 2014..

Gabanin tattaunawar ta yau shugaba Joe Biden na Amurka ya nanata cewa, sun cimma matsaya da Vladimir Putin kan cewa Rasha ba za ta yiwa Ukraine mamaya ba.

Haka zalika tattaunawar shugabannin biyu na zuwa a dai dai lokacin da Sojin Ukraine guda ya rasa ransa a wani yaki takanin dakarun kasar da ‘yan awaren yankin gabashi masu samun goyon bayan Rasha.

Sanarwar rundunar Sojin kasar ta ce baya ga soji guda da ya rasa ransa akwai kuma wani daban da ya samu rauni a wasu mabanbantan hare-hare har 3 da ‘yan awaren suka kai kansu cikin sa’o’i 24.

Zuwa yanzu rikicin na gabashin Ukraine tsakanin dakarun gwamnati da 'yan awaren da ke samun goyon bayan Rasha ya hallaka mutane akalla dubu 13 ko da ya ke bangarorin biyu na shirin cimma jituwa don farfado da yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.