Isa ga babban shafi
Amurka-Capitol

Biden ya yi gargadi kan barazanar siyasar zub da jini a Amurka

Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi gargadi kan yadda magoya bayan tsohon shugaba Donald Trump ke barazanar mayar da siyasar kasar mai cike da rikici da zub da jini, kalaman da ke zuwa dai dai lokacin da ake cika shekara guda da farmakin Capitol da ya hallaka mutane 5.

Joe Biden na shirin gabatar da jawabi na musamman kan cika shekara guda da rikicin na Capitol.
Joe Biden na shirin gabatar da jawabi na musamman kan cika shekara guda da rikicin na Capitol. © REUTERS
Talla

Shugaba Joe Biden wanda ke wannan gargadi gabanin jawabi na musamman da zai gabatar yau alhamis game da cika shekara guda da rikicin irinsa na farko da kasar ta gani, ya ce sam bai kamata siyasar kasar ta zama mai cike da zub da jini ba.

Kalaman na Joe Biden na zuwa ne kwana guda bayan da babban alkalin kasar Merrick Garland ya sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a farmakin na Capitol bayan matsin lamba daga jam’iyyar Democrat da ke ganin wajibi ne babban alkalin ya yi amfani da karfin ikonsa wajen hukunta masu hannu a rikicin.

Fiye da mutane 725 ake tuhuma da laifin tayar da tarzomar da kuma haddasa rikici baya ga farmakar jami’an tsaron na Capitol ciki har da 165 da aka samu da laifi aka kuma aike da 70 gidan yari.

A ranar 6 ga watan janairun 2021 ne makwanni 2 gabanin rantsar da Joe Biden bayan zaben da ya kayar da Donald Trump, magoya bayan shugaban mai barin gado a wancan lokaci suka farmaki ginin na Capitol mai dauke da ginin majalisun kasar bayan wani jawabinsa da ke nuna yadda aka yi magudi kan nasararsa a zaben kasar.

Acewar Merrick Garland sashen shari’a na Amurka ya na bibiyar rikicin sau da kafa kuma zai hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikinsa ko da a kowanne mataki ya ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.