Morocco za ta fara jigilan Jiragen Sama zuwa Israila don maido da zumunci
Kamfanin Jiragen Sama na kasar Morocco, Royal Air Maroc (RAM) sun sanar da cewa za su fara jigilan matafiya ta jiragen sama zuwa Isra'ila, shekara daya bayan da kasashen biyu suka maido da dasawa.
Wallafawa ranar:
Ana sa ran fara jigilan fasinja tsakanin Casablanka da Tel Aviv ranar 12 da watan gobe, kwanaki biyu bayan cika shekara daya da maido da zumunci tsakanin kasashen biyu karkashin su.
A cewar kamfanin jiragen saman za su rika jigila sau uku cikin mako daya, kafin a sami jigila sau uku a mako.
Tun shekara ta 1993 Morocco da Isra'ila suka kulla zumunci, amman kuma Morocco ta janye sakamakon rikicin intifada na Palestinawa a shekara ta 2000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu