Kotun Morocco ta daure wani dan jarida shekaru 5 a gidan yari
Kotun Morroco ta yanke dan jaridar kasar Soulaimane Raissouni hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari saboda samunsa da lafin cin zarafin wani mutum.
Wallafawa ranar:
Raissouni, wanda ya kwashe kwanaki 93 yana yajin cin abinci, bai halarci zaman kotun ba.
Dan jaridar mai shekaru 49 ya kasance a tsare tun cikin watan Mayun shekarar da ta gabata bayan da wani mai rajin kare hakkin masu auren jinsi ya zarge shi da cin mutunci, zargin da ya musanta.
Magoya bayan Raissouni wanda babban edita jaridar Akhbar Al Yaoum sun alakanta shariar da hana ‘yan jaridu gudanar da ayyukansu, ko da yake gwamnati na cewa bangaren shari’arta mai zaman kansa ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu