Isa ga babban shafi
Morocco-Tabar wiwi

Morocco za ta halasta amfani da tabar wiwi a bangaren lafiya

Morocco na daf da sahale amfani  da tabar wiwi a bangaren lafiya, bayan da gwamnatin kasar ta amince da wani kudirin doka mai nasaba da hakan.

Wasu kasashen duniya sun fara halasta tabar wiwi.
Wasu kasashen duniya sun fara halasta tabar wiwi. GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP/File
Talla

Sai dai a wannan makon, gwamnatin ta jaddada haramcin amfani da tabar don nishadi, kuma kudirin dokar amincewa da ita wajen samar da waraka na bukatar sahalewar majalisar dokoki.

Kudirin dokar da gwamnatin kasar ta gabatar na nuni da cewa matakin zai sauya aikin noman tabar wiwi zuwa wanda doka ta amince da ita, ya kuma maishe ta wata kafa ta samar da ayukan yi.

A cewar wani rahoton ofishin majalisar dinkin duniya mai sa ido a kan kwayoyi da aikata muggan laifuka, Morocco da ke arewacin Afrika ce kasar da ta fi samar da wiwi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.