Isa ga babban shafi
SAUYIN-YANAYI

Kasashen Afirka sun bukaci biliyoyin daloli a matsayin diyya

Kasashen Afirka dake fama da illar da matsalolin sauyin yanayin da basu suke haifarwa a duniya ke samarwa, da suka hada da fari da ambaliya da kuma yunwa, na bukatar diyyar biliyoyin daloli a wajen taron sauyin yanayin dake gudana a Glasgow da aka yiwa lakabi da COP26.

Shuagban Kungiyar kasashen Afirka ta AU Felix Tshisekedi tare da Firaministan Birtaniya Boris Johnson da shugaban Amurka Joe Biden
Shuagban Kungiyar kasashen Afirka ta AU Felix Tshisekedi tare da Firaministan Birtaniya Boris Johnson da shugaban Amurka Joe Biden Erin Schaff Pool/AFP
Talla

Mutane da dama na kallon wannan taron a matsayin wani yunkuri na karshe da ya ragewa shugabannin kasashen duniya wajen daukar matakan ceto Bil Adama da muhallin su daga tabarbarewa.

Abinda ya rataya akan kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya shine batun rage sinadarin da suke fitarwa wadda ke haifar da gurbacewar muhallin da aka akalla maki guda da rabi a ma’aunin salsas, kamar yadda ake da shi kafin shekarun da aka samu karuwar masana’antu a duniya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Yarima Charles da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma shugaban Mauritania Mohammed Ould Ghazouani
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Yarima Charles da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma shugaban Mauritania Mohammed Ould Ghazouani © Buhari Sallau

Amma ga kasashe irin na Afirka, babban abinda ke gaban su shine samun isassun kudaden da zasu yi amfani da su wajen bunkasa tattalin arzikin su wadanda suka gamu da koma baya sakamakon gurbacewar muhallin, tare da kuma samar da yanayin da za’a ci gaba da rayuwa da matsalolin da ake fuskanta.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU kuma shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Felix Tshisekedi yace nahiyar Afirka ba zata iya shawo kan wadannan matsaloli ita kadai ba.

Yayin gabatar da jawabin sa ga wakilan kasashen duniya dake halartar taron a Glasgow, Tshisekedi ya bayyana cewar a matsayin nahiyar wadda ke haifar da kashi 3 kacal na sinadarin dake gurbata muhallin, bai dace a bar ta ta samarwa kan ta mafita ba.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da shugaban Bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da shugaban Bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina © Niger Presidency

Kasashen duniya masu arziki a shekarar 2009 sun yi alkawarin baiwa kasashe matalauta akalla Dala biliyan 100 kowacce shekara domin rage radadin illar sauyin yanayin da suke fama da shi, amma kuma har ya zuwa wannan lokaci wannan alkawari na nan a matsayin mafarki, yayin da kasashe irin su Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Nijar da kuma Madagascar ke fuskantar matsalar ambaliya da kuma fari.

Shugaban Madagascar Andry Rajoelina ya bayyana akalla mutane sama da miliyan guda da dubu 300 a kasar sa ke fuskantar yunwa sakamakon illar da sauyin yanayi ya haifar musu.

Yanzu haka Bankin Raya kasashen Afirka na AfDB da kuma wata Cibiya dake Netherlands sun kaddamar da shirin amfani da Dala biliyan 25 domin taimakawa irin wadannan kasashe, kuma ya zuwa wannan lokaci kasashen Afirka sun karbi kusan rabi daga cikin wadannan kudade domin amfani da su, sai dai shugaba Tshisekedi na cewa kudin basu isa ba, saboda haka ya dace manyan kasashen duniya su kara kudaden.

Shugaban Amurka Joe Biden ya cacaki China akan kauracewa taron sauyin yanayi
Shugaban Amurka Joe Biden ya cacaki China akan kauracewa taron sauyin yanayi REUTERS - POOL

Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka na AfDB Akinwumi Adeshina ya bukaci kashe Karin kudade domin shawo kan matsalolin da sauyin yanayin ke haifarwa domin rage radadin sa.

Shugaban taron Alok Sharma ya amince da matsalolin da aka samu wajen gibin bada kudaden, inda ya sanar da bada Dala miliyan 197 ga kasashen Afirka daga Birtaniya domin taimaka musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.