Isa ga babban shafi
Duniya - Gurbatacciyar iska

Gurbatacciyar iska na kashe mutane miliyan 7 duk shekara - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta karfafa matakan da ta tsara domin tsaftace iskar da dan Adam ke shaka, inda ta bayyana gurbatacciyar iskar a matsayin barazana mafi girma ga lafiya a yanzu haka, wadda kuma ke lakume rayukan mutane akalla miliyan 7 a duk shekara.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce gurbacewar iska na halaka mutane akalla miliyan 7 a duk shekara.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce gurbacewar iska na halaka mutane akalla miliyan 7 a duk shekara. NIKOLAY DOYCHINOV AFP/File
Talla

A yanzu haka dai WHO ta yi gyara ga kusan dukkanin matakan tsaftace iskar da muke shaka zuwa kasa da kason da ta dibar musu a baya, tare da gargadin cewa, muddin hukumomin kasashe da sauran masu ruwa da tsaki suka gaza kiyaye su, to fa sakamakon da za a gani ba mai kyau bane musamman ga lafiyar dan Adam.

Sabbin manufofin yaki da matsalar ta gurbatar iskar ana zuwa ne a daidai lokacin ake shirin gudanar da taron kasashen duniya kan canjin yanayi a Glasgow da ke kasar Scotland daga ranar 31 ga Oktoba zuwa 12 ga Nuwamba.

Idan za a iya tunawa dai, rabon da hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da sabbin matakan dakile gurbatar iska tun a shekarar 2005, wadanda suka yi tasiri akan manufofin rage matsalar a sassan duniya.

Sai dai, a cikin shekaru 16 da suka gabata, hukumar WHO ta ce karin shaidun da ta samu na nuna cewa matsalar ta gurbacewar iskar na shafar lafiyar dan adam tun daga matakai mafiya kankanta, sabanin fahimtar da kwararrun ta suka yi a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.