Isa ga babban shafi
CUTAR-KANSA

Hukumar Lafiya ta bukaci kara harajin barasa a Turai

Hukumar Lafiya ta duniya ta bada shawarar ribanya harajin da kasashen Turai ke sakawa akan barasa ko kuma giya a yankin domin ceto rayukan mutane kusan 5,000 dake mutuwa sakamakon harbuwa da cutar kansa ko kuma sankara kowacce shekara.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus AP - Balazs Mohai
Talla

Ofishin Hukumar dake kula da nahiyar Turai yace kara harajin da ake karba akan giyar na daya daga cikin manyan hanyoyin da zasu kare jama’a daga kwankwadar giyar suna kuma kamuwa da cutar a kasashen dake nahiyar.

Hukumar tace shan giya na da nasaba da harbuwa da cututtuka da dama da suka hada cutar koda da sanakara mama da kuma ciwon hanta.

Sanarwar hukumar yace daukar wannan mataki na iya kare akalla mutane 10,700 daga kamuwa da cutar kansa da kuma hana 4,850 daga mutuwa daga cututtukan dake da nasaba da ita.

Shugabar gudanarwar kungiyar Turai Ursula von der Leyen
Shugabar gudanarwar kungiyar Turai Ursula von der Leyen AFP - YVES HERMAN

Hukumar tace an samu karuwar kashi 6 na mutanen dake harbuwa da cutar kansar da kuma masu mutuwa a nahiyar dake da kasashe 53 da kuma wasu yankuna cikin su harda Rasha da wasu kasashen dake tsakiyar Asia.

Ofishin hukumar yayi hasashen cewar ana iya samun masu kamuwa da cutar kansa 180,000 kowacce shekara da kuma 85,000 dake mutuwa sakamakon shan giya kawai.

Hukumar ta bayyana cewar harajin da aka dorawa barasa da kuma dangoginta a nahiyar Turai ya gaza, saboda haka tana bada shawarar ribanya shi yadda zai hana wasu mutane samun ta cikin sauki domin kare lafiyar su.

Mujallar ‘The Lancet‘ ta Lafiya da ake wallafawa a Birtaniya tace kasashen Rasha da Birtaniya da kuma Jamus na iya kare lafiyar mutane 725,000 da kuma hana 525 mutuwa idan sun yi amfani da shawarar da aka basu na kara yawan harajin, ganin yadda aka samu sabbin masu kamuwa da cutar kansa miliyan 4 da dubu 800 a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.