Isa ga babban shafi
GOBARA

Gobara ta kashe firsinoni 41 a Indonesia

Wata gobara da ta tashi a gidan yarin kasar Indonesia dake Tsibirin Java tayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 41, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Taswirar Indonesia
Taswirar Indonesia © Reuters
Talla

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne a gidan yarin dake wajen birnin Jakarta lokacin da firsinoni ke barci, abinda ya sa ta yiwa da dama daga cikin su matukar illa.

Hotunan da aka nuna ta kafar talabijin lokacin da gobarar ke ci, na dauke da yadda wutar ta kama gadan gadan ta kuma mamaye wani ginin dake cikin gidan yarin, yayin da jami’an kashe gobara ke kokarin shawo kan ta.

Shugaban Yan Sandan Jakarta, Fadil Imran ya tabbatar da mutuwar mutane 41, wasu 8 kuma sun samu munanan raunuka, yayin da wasu 72 suka samu raunukan da basu da hadari.

Imran yace yana zaton gobarar ta tashi ne daga wutar lantarki, amma tuni hukumomin kasar suka bada umurnin  gudanar da bincike akan abinda yayi sanadiyar tashin ta.

Gidan yarin dai na dauke da firsinonin da suka wuce kima da suka kai kusan 270,000, yayin da yake kuma fama da rashin tsafta da kuma matsalar yadda wasu daga cikin wadanda ake tsare da s uke tserewa.

Ko a shekarar 2019 sanda aka samu akalla firsinoni 100 da suka gudu daga gidan yarin Yankin Riau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.