Isa ga babban shafi
Indonesia - Coronavirus

Indonesia: Korona ta lakume rayukan mutane fiye da dubu 1 a rana guda

Gwamnatin kasar Indonesiya ta dada karfafa matakan kariyar da take dauka wajen yaki da annobar Covid-19 a kasar lura da yadda mutane sama da dubu 1 ke mutuwa a kasar cikin awowi 24.

Wasu Iyalai cikin jimamin dan uwansu da annobar Korona ta kashe, bayan jana'izarsa a daya daga cikin makabartun dake birnin Jakarta.
Wasu Iyalai cikin jimamin dan uwansu da annobar Korona ta kashe, bayan jana'izarsa a daya daga cikin makabartun dake birnin Jakarta. © AP
Talla

Sabbin matakan takaita walwalar jama’a za su shafi birane da yawa kama daga tsibirin Sumatra dake yamma zuwa gabashin Papua, bayan da sabon nau’in cutar Covid-19 din wato Delta mafi hatsari ya fara yaduwa a Kudu maso Gabashin Asiya.

Asibitoci da dama yanzu haka sun fara kauracewa karbar marasa lafiya, lamarin da ake ganin jami’an lafiya na barin mutane suna mutuwa a gida, yayin da ma’aikatan makabartu ke kai kawo wajen binne gawarwakin da ke ci gaba da karuwa.

Tuni dai hukumomi suka bada umarnin rufe masallatai, wuraren shakatawa, manyan shaguna da gidajen cin abinci a Jakarta da tsibirin Java gami da sauran wuraren kai kawon jama’a.

Amma rahotanni na cewa akwai  wadanda suka yiwa dokar karan tsaye, bayan da wasu ma’aikatu aka bude su hadi da shaguna, duk da gargadin da hukumomi suka yi.

Indonosia wadda ta kasance kasa ta huɗu mafi yawan jama'a a duniya ta wallafa rahoton da ya nuna cewa sabbin alkaluman wadanda suka harbu da cutar Korona a kasar ya karu zuwa dubu 34 da 379, daga cikinsu kuma dubu 1 da 40, wanda ya ninka sau 10 na yawan mace-mace a kowace rana kasa da wata guda da ya gabata a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.