Isa ga babban shafi
Indonesiya

Daukacin ma'aikata 53 na jirgin ruwan Indonesia da ya bace sun mutu

Rundunar sojin Indonesia ta sanar a Lahadin nan cewa dukkanin ma’aikatan jirgin ruwan karkashin ruwan nan nata da ya bace a makon da ya gabata sun mutu, jim kadan bayan da ta tabbatar da cewa an gano tarkacen jirgin a gabar ruwa.

Hukumomin Indonesia sun ce daukacin ma'aikatan jirgin ruwan karkashin ruwa da ya bace sun mutu.
Hukumomin Indonesia sun ce daukacin ma'aikatan jirgin ruwan karkashin ruwa da ya bace sun mutu. Handout INDONESIA MILITARY/AFP/File
Talla

Hukumomi sun ce da sanyi safiyar Lahadin nan ne suka hango wasu alamu daga wani bangaren tekun Bali mai zurfin mita 800, wato fiye da iya zurfin da jirgin KRI Nanggala 402 zai iya jurewa.

Wanna  na zuwa ne bayan da sojin ruwan kasar ta Indonesia suka tabbatar da cewa sun gano karikitan jirgin, sun a mai ayyana cewa nutsewa  jirgin ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.