Isa ga babban shafi
IMF-Tattalin arziki

Asusun lamuni na duniya zai ba kasashe matalauta rance maras ruwa

Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya sanar da cewa ya amince da kara wa kansa karfin iko wajen samar da rance maras ruwa ga kasashe marasa karfin tattalin arziki, da zummar taimaka musu wajen farfadowa daga radadin tattalin arziki da ya kama su samakon bullar annobar Coronavirus.

 shugabar Asusun Bada Lamuni na Duniya Kristalina Georgieva.
shugabar Asusun Bada Lamuni na Duniya Kristalina Georgieva. NICHOLAS KAMM AFP/File
Talla

Asusun bada lamunin ya ce annobar Covid-19 ta zuke kudaden da aka tanadar wa wadannan kasashe, wadanda akasarinsu ke yankin Kudu da saharar Afrika fiye da yadda ya yi tsammani, kuma a halin da ake ciki su na cikin tsananin bukata.

Sauye sauyen da asusun ya amince da su a ranar 14 ga watan Yuli sun hada da karin kashi 45 na iyakancewar da aka yi a kan karbar rance, kana ya cire ilahirin shamaki da ke tattare da samun rance ga kasashe marasa karfi.

Asusun ya kara yawan kudaden da ya ke bayarwa ga kasashe matalauta a shekarar da ta gabata har ninki 8 fiye da yadda ya ke a shekaru 3 da suka wuce, kuma ya ce akwai hasashen cewa bukatu za su ci gaba da karuwa tsawon shekaru.

Zalika, asusun bada lamunin na duniya yana aiki tukuru wajen habaka samar da kudade ga gidauniyarsa ta rage radadin talauci da ci gaban kasashe don samar da rancen da babu ruwa, yana mai kira ga karin dala biliyan 4 daga kasashen da ke cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.