Hukumomin tsaron duniya sun cafke daruruwan masu kutse a wayoyin jama'a
Hukumomin tsaron duniya sun sanar da wani gagarumin aikin da suka kwashe shekaru 3 suna yi wanda ya kai ga kama daruruwan mutanen da ke kutse cikin wayoyin jama’a, suna aikata laifuffuka a duniya.
Wallafawa ranar:
Aikin da aka gudanar a kasashe 16 na duniya ya bada damar gano masu aikata laifuffuka da kungiyoyi dake mu’amala da makamai da masu safarar miyagun kwayoyi da halarta kudaden haramun da makamantan su.
Firaministan Australia Scott Morrison ya bayyana kaduwar sa da lamarin, bayan gurfanar da irin wadannan mutane 224 a kasar sa.
‘Yan sanda Australia sun ce gaba daya mutane 224 din sun fuskantar tuhume tuhume har dari 5 a gaban kuliya.
‘Yan sanda New Zealand sun bayyana cewa samamen da aka shi ne mafi inganci da armashi a da watab hukuma ta taba kai wa a duniya ya zuwa yanzu.
An ci gaba da kama masu laifi, kuma ana sa ran sanar da duniya su, a cewar ‘yan sandan Australia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu