Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Majalisar Birtaniya na son a binciki kutsen da Rasha ta yi kasar

Majalisar Birtaniya ta bukaci gwamnatin kasar ta binciki zargin kutsen Rasha a zaben raba gardamar ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai da ya gudana cikin shekarar 2016.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson a zauren Majalisar Dokokin Kasar
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a zauren Majalisar Dokokin Kasar PRU / AFP
Talla

Rahoton da Majalisar ta fitar a wannan Talata ya nuna yadda wasu makusantan shugaba Vladimir Putin na Rasha suka taka rawar gani yayin zaben raba gardamar ficewar Birtaniyar daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Wani mamban kwamitin kwararru na Majalisar Birtaniyar Kevan Jones ya yi zargin cewa duk da samun wadatattun hujjojin da ke nuna rawar da Rashar ta taka a 2016, gwamnati ta gaza kaddamar da bincike don daukar matakan da suka kamata.

Sai dai rahoton kwamitin kwararru na Majalisar ya ce, rashin gano gamsasshiyar hujja game da kutsen na Rasha a zaben raba gardamar da zaben neman ‘yancin Scotland daga Birtaniyar a 2014, ya faru saboda gwamnati ta yi gum da bakinta.

A cewar dan majalisar Jones ko shakka babu kutsen Rasha a al’amuran Birtaniya ba sabon abu ba ne wanda ke nuna cewa ya zama wajibi a gabatar da sakamakon binciken don daukar matakan da suka kamata.

Sakamakon zaben raba gardamar ficewar ta Birtaniya daga EU ya nuna kashi 55 na al’ummar kasar na son fita, yayin da kashi 45 ke son aci gaba da zama a EU, sai dai babu cikakken bayani kan ko wanne bangare Rashar ta goya wa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.