Isa ga babban shafi
Amurka-Tusla

Kisan gilla ne karara ya faru a Tusla shekaru 100 da suka gabata- Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya zama shugaba na farko da ya halarci bikin tuna kisan gillar da aka yiwa bakaken fata a Tusla da ke jihar Oklahoma shekaru 100 da suka gabata sakamakon tashin hankalin da wasu fararen fata suka haifar.

Shugaba Joe Biden yayin jawabinsa a taron jimamin cika shekaru 100 da kisan gillar da aka yiwa bakaken fata a Tulsa.
Shugaba Joe Biden yayin jawabinsa a taron jimamin cika shekaru 100 da kisan gillar da aka yiwa bakaken fata a Tulsa. REUTERS - CARLOS BARRIA
Talla

Yayin jawabin sa mai sosa rai, Biden ya ce abinda ya faru a shekarar 1921 kisan gilla ne karara, wanda aka nemi boye shi saboda kada Duniya ta sani.

A ranar 31 ga watan Mayun shekarar 1921 wata tawagar bakaken fata ta ziyarci kotun Tusla domin kare wani bakar fata da ake zargin da cin zarafin wata farar fata, abinda ya bai wa taron daruruwar farar fatar damar harbi wanda ya tilastawa bakaken fatar janyewa zuwa unguwannin su.

Kwana guda bayan haka, fararen fatar da asuba suka kai hari unguwannin bakaken fatar inda suka sace kayayyaki da kona gidaje a rikicin da ya lakume rayukan bakaken fata akalla 300 da kuma sanya sama da dubu 10 asarar gidajen su.

A watan Afrilun da ya gabata, wasu daga cikin wadanda suka tsira daga tashin hankalin sun gabatar da shaidu a Majalisar dokoki inda suka bukaci Amurka ta amince da irin ukubar da suka gani.

A shekarar 2001 an kafa hukumar binciken kan kisan gillar wanda ya bada umurnin biyan diyya ga mazauna unguwar Greenwood da aka yiwa kisan gillar, amma har ya zuwa wannan lokaci ba’a biya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.