Isa ga babban shafi
India

Shekaru 70 da kisan gillar da aka yiwa Mahatma Gandhi

Yau ake cika shekaru 70 da kisan gillar da aka yiwa Mahatma Gandhi, mutumin da ake yiwa kallon uba ga daukacin yan kasar India.An dai haifi Gandhi ne ranar 2 ga watan Oktoban 1869 a matsayin Mohandas Karamchand Gandhi a Porbardar dake Jihar Gujarat.

Mahatma Gandhi, mutumin da ake yiwa kallon uba ga daukacin yan kasar India.
Mahatma Gandhi, mutumin da ake yiwa kallon uba ga daukacin yan kasar India. Getty-Dinodia Photos / Contributeur
Talla

Iyayyen sa sun masa aure yana da shekaru 13 tare da Kasturba Makanji wanda suka haifi yara hudu tare.

Ya karanta aikin lauya a London tsakanin shekarar 1888 zuwa 1891, kana yayi aikin lauya a Afrika ta kudu tsakanin shekarar 1893 zuwa 1915.

A shekarar 1922 a matsayin jigo na jam’iyyar NCP yayi kiran bijirewa turawan Birtaniya dake mulkin India abinda ya sa aka kama shi aka daure na shekaru biyu.

A shekarar 1930 ya jagoranci wata zanga zangar da aka yiwa lakabi da ‘Salt March’ daga Ahmedabad abinda ya sa aka sake kama shi aka tsare.

A shekarar 1942 ya kira yajin aikin gama gari dan tilastawa turawan Birtaniya ficewa daga India abinda ya sa aka kama shi aka tsare har zuwa shekarar 1944.

India ta samu yanci a shekarar 1947, yayin da aka yiwa Mahatma Ghandi kisan gilla ranar 30 ga watan Janairu shekarar 1948, kuma mutane sama da miliyan biyu ne suka halarci jana’izar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.