Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

'Yan sandan Isra'ila sun harbe Bafalasdine a yamma da kogin Jordan

Ma’aikatar lafiyar yankin Falasdinu ta ce jami’an tsaron Isra’ila sun kashe wani Bafalasdine a gabar yamma da kogin Jordan.

Tutar yankin Falasdinu a kusa da gidajen Yahudawa ta gina a kauyen An-Naqura dake kusa da birnin Nablus, a yankin gabar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye. 29/5/2021.
Tutar yankin Falasdinu a kusa da gidajen Yahudawa ta gina a kauyen An-Naqura dake kusa da birnin Nablus, a yankin gabar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye. 29/5/2021. REUTERS - RANEEN SAWAFTA
Talla

Lamarin ya auku ne a yayin da arrangama ta kaure tsakanin ‘yan sandan na Isra’ila da Falasdinawan dake zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin Isra’ilar na sake mamaye wasu karin yankunansu don gina gidajen ‘yan kama wuri zauna a kauyen Beita dake birnin Nabulus.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar falasdinawan dake zanga-zangar sun yi amfani da duwatsu wajen jifan ‘yan sanda abinda ya sanya su maida martani ta hanyar bude musu wuta.

Tun a shekarar 1967 Isra'ila ta mamaye yankin yamma da kogin Jordan tare da zirin Gaza, yayin yakin da ta gwabza da Falasdinawa masu samun goyon bayan wasu kasashen Larabawa tsawon kwanaki 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.