Isa ga babban shafi
Faransa - Gaza

Faransa ta gabatarwa MDD kudurin neman fitar da sanarwa kan rikicin Gaza

Kasar Faransa ta gabatar da kudirin dake bukatar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince da sanarwa kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa, kwanaki 8 bayan da Amurka ta hau kujerar naki.

Birnin Gaza yayin da Isra'ila ke kai hare-hare kan Falasdinawa. 17/5/2021.
Birnin Gaza yayin da Isra'ila ke kai hare-hare kan Falasdinawa. 17/5/2021. AP - Hatem Moussa
Talla

Wannan ya biyo bayan tattaunawar da shugaba Emmanuel Macron da yayi da takwaran sa na Masar AbdulFatah al-Sisi da kuma Sarki Abdallah na Jordan.

Jakadan China a Majalisar Zhang Jun ya bayyana cewar suna goyan bayan duk wani shirin kawo karshen wannan rikici domin tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Yadda tankokin yankin Isra'ila ke harba bama-bamai ta kasa akan birnin Gaza.
Yadda tankokin yankin Isra'ila ke harba bama-bamai ta kasa akan birnin Gaza. AP - Yonatan Sindel

Mujallar Times of Israel da ake wallafa ta a Isra’ila ta ruwaito cewar rundunar sojin saman kasar ta jefa bama-bamai har 122 kann birnin Gaza a cikin mintuna 25 a daren ranar Talata, a cigaba da hare-haren da take kaiwa kan Falasdinawa.

Kawo yanzu Falasdinawa akalla 219 dakarun Isra’ila suka kashe, cikinsu har da yara 63, yayin da wasu kimanin dubu 1 da 500 suka jikkata, tun bayan kaddamar da hare-haren da sojojin suka yi kan birnin Gaza daga ranar 10 ga watan Mayu.

A isra’ila kuwa, hukumomin kasar sun bayyana mutuwar mutane 12 tare da jikkatar wasu 300, sakamakon hare-haren makaman rokar da mayakan Hamas suke harbawa kann sassan biranen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.