Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Shugabanni sun koka kan tsanantar rikicin Isra'ila da Falasdinu

Shugabanni a sassan duniya na cigaba da yin tsokaci kan yadda rikicin na Falasdinawa da Isra’ila ke cigaba da tsananta ba kuma tare da alamun kawo karshensa a nan kusa ba.

Dakarun Isra'ila yayin luguden wuta kan Falasdinawa a birnin Gaza.
Dakarun Isra'ila yayin luguden wuta kan Falasdinawa a birnin Gaza. AP - Ariel Schalit
Talla

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, ofishin jakadancin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci bayanai daga shugaban Amurka Joe Biden kan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa fararen hula. Ita kuwa shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya Michelle Bachelet kokawa tayi kan yadda shugabannin Isra’ila da Falasdinawa ke furta kalaman tunzuri a maimakon soma lalubar hanyar warware kazamin yakin da ya barke.

Kamfanin dillancin labarai na AP da talabijin ta Aljazeera kuwa bayyana kaduwa suka yi kan yadda Isra’ila ta rusa ofisoshinsu da na sauran kafafen yada labarai da gangan duk da cewar sun dade da sanin inda suke da kuma ayyukansu.

Kakakin shugaban Turkiya Fahrettin Altun
Kakakin shugaban Turkiya Fahrettin Altun © TRTWorld

Shi kuwa kakin shugaban Turkiya Fahrettin Altun Allah-wadai yayi da farmakin da Isra’ila ta kaiwa kafafen yada labarai yayi, abinda ya bayyana a matsayin babban koma baya ga ‘yancin manema labarai.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Nicholas Kamm AFP/File

Shugaban Amurka Joe Biden da ya gana da Fira Minista Netanyahu ta wayar tarho, ya bayyana damuwa kan tsanantar rikicin, tare da nemarwa manema labarai kariya, yayin da shi kuma jagoran kungiyar mayakan Hamas na Isma’ila Haniya ya shaidawa wani taron gangami cewar ba za su daina harba rokoki kan Isra’ila ba har sa dakatar da kaiwa musu farmaki.

Daga karshe kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da su gaggauta kawo karshen hare-haren da Isra’ila da Falasdinawa ke kaiwa juna, yayin da kuma tayi Allah-wadai da laifukan yakin da ake aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.