Isa ga babban shafi
IRAN

An kai hari kan tankar Iran a gabar ruwan Syria

Akalla mutane uku sun mutu lokacin da aka kai hari kan tankar Iran a kusa da gabar ruwar Syria jiya Asabar,  hari na irinsa na farko da aka gani tun lokacin da yakin ya barke a kasar shekaru goma da suka gabata.

Shugaban Iran Hassan Rouhani yayin ganawa da majalisar ministocin kasar a Tehran, 14, ga watan Afrelu 2021.
Shugaban Iran Hassan Rouhani yayin ganawa da majalisar ministocin kasar a Tehran, 14, ga watan Afrelu 2021. AP
Talla

Rami Abdel Rahman, shugaban kungiyar Kare Hakkin Dan Adam dake sa’ido kan rikicin Siriya yace, mutane ukun da suka mutu 'yan kasar ta Syria ne ciki har da ma'aikata biyu" a harin wanda ya haifar da gobara.

Jami’in yace ba’asan wanda ya kai harin ba, kuma ko anyi amfani da jirgin sama mara matuki ne ko kuma anyi amfni da makami mai linzami wajen kai hari kan tankar mai da ya taso daga Iran kuma bai nisa da tashar jiragen ruwan Banias ba lokacin da lamarin ya auku, kuma babu tabbas ko Isra’ila ta kai shi.

To sai dai Kamfanin dillacin labarai na kasar SANA, ya ambato ma’aikatar man fetur din kasar na cewa gobarar ta tashi ne bayan “abin da ake zaton hari ne ta jirgi mara matuki da ya taso daga ruwan Labanon”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.