Isa ga babban shafi
Lafiya-Amnesty

Amnesty ta zargi manyan kasashe da gazawa wajen hadin kan Duniya

Kungiyar Amnesty International ta zargi manyan kasashen Duniya da gazawa wajen hadin kai domin shawo kan annobar corona sakamakon yadda su ke ci gaba da boye rigakafin cutar wanda har yanzu ya kasa kai wa ga wasu kasashe matalauta.

Shugabar kungiyar Amnesty International Agnès Callamard.
Shugabar kungiyar Amnesty International Agnès Callamard. © RFI/Véronique Gaymard
Talla

Rahotan shekara-shekara na kungiyar ya ce annobar corona ta bankado rashin hadin kan da ke tsakanin kasashen Duniya, yayin da ta zargi China da wasu kasashe da ke amfani da annobar korona wajen take hakkin Bil Adama.

Sakatare Janar na Kungiyar Agnes Callamard wadda ta yi mummunar suka kan yadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fitar da kasar daga Hukumar lafiya ta ce matakan da kasashe masu arziki ke dauka na babakere kan magungunan rigakafin ya sanya kananan kasashe shiga tasku wajen tinkarar annobar.

Coronavirus na ci gaba da haddasa asarar dimbin rayuka a sassan Duniya, inda a baya-bayan an cikin kasashen Matalauta Kamaru ke matsayin kan gaba a jerin wadanda cutar ke tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.