Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta yi tir da harin da aka kaiwa 'yan Kasuwa a Ibadan

Kungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da harin da aka kaiwa yan kasuwa a Kasuwar Ibdana wanda yayi sanadiyar rasa rayuka.

Kungiyar kare hakkin bil'ada ta Amnesty International
Kungiyar kare hakkin bil'ada ta Amnesty International @សហការី
Talla

Kakakin kungiyar Isa Sanusi ya shaidawa kamfanin yada labaran AFP cewar an kai harin kan Yan kasuwar ne ranar juma’ar da ta gabata, a kasuwar Sasa kuma an samu rasa rayuka, duk da yake basu iya tantance yawan mutanen da suka mutu ba.

Kamfanin AFP yace a cikin makwannin da suka gabata, ana fama da kalamun batunci da ake yiwa Yan arewacin kasar da kuma kai hare hare kan matsugunan Fulani makiyaya da ake zargi da aikata laifuffuka a Yankin Jihohin Yarbawa.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi Allah wadai da tashin hankalin, inda ya bukaci hukunta masu aikata laifuffuka ba tare da shafawa wata kabila karar tsana ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.