Kurdawa sun kame gwamman mayakan IS a Syria
Dakarun sa kai na Kurdawa a Syria, sun bayyana kame akalla mutane 125 da suke tuhuma da zama mayakan kungiyar IS.
Wallafawa ranar:
Kurdawan sun kame gwamman mutanen ne, bayan samamen da suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Hol dake arewa maso gabashin Syria.
Kakakin mayakan sa kan Kurdawa a karkashin kungiyar SDF Ali al-Hassan, ya ce zarginsu ya yi karfi ne bayan da alkaluma da suka nuna daga farkon shekarar nan zuwa yanzu an yiwa mutane akalla 47 kisan gilla a sansanin na Al-Hol.
Kurdawan dai sun dade suna zargin cewa akwai mayakan IS dake boye a sansanin mai dauke da ‘yan gudun akalla dubu 62.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu