Sojojin Rasha sun kashe mayakan IS da dama a Syria
Sojojin Rasha su halaka mayakan kungiyar IS akalla 21 a yankin hamadar kasar Syria dake lardin Dier Ezzor.
Wallafawa ranar:
Cibiyar Syrian Observatory dake sa ‘ido kan yakin kasar, tace dakarun na Rasha sun halaka mayakan na IS ne bayan luguden wuta sama da 130 da jiragen yaki suka yi kan wasu yankunan kasar ta Syria, dake zama maboyar ragowar mayakan na IS.
A shekarar 2014, kungiyar IS ta mamaye yankuna masu yawan a kasashen Syria da Iraqi, wanda daga bisani, rundunaonin sojin hadin gwiwa sun samu nasarar tarwatsa kungiyar.
Sai dai wani rahoton majalisar dinkin duniya, a baya bayan nan ya ce har yanzu akwai ragowar myakan IS kimanin dubu 10 a wasu yankunan Syria da Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu