Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Matakin Iran kan Nukiliya ya mamaye babban taron hukumar IAEA

Matakin da Iran ta dauka a baya bayan nan na takaita aikin masu bincike na Hukumar da ke sa ido a kan makamashin nukiliya ta majalisar Dinkin Duniya ya kasance babban maudu’in taron Majalisar gudanawar hukumar da ya gudana yau Litinin.

Ziyarar shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi a Iran don duba sabbin sauye-sauyen da kasar ta samar a fannin Nukiliya. Atomic Energy
Ziyarar shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi a Iran don duba sabbin sauye-sauyen da kasar ta samar a fannin Nukiliya. Atomic Energy VIA REUTERS - WANA NEWS AGENCY
Talla

Kasashen yamma za su ci gaba da sa ido tare da dakile Iran a  kan wannan batu ta hanyar da ba za ta jefa kokarin da ake na farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 tsakaninta da manyan kasashen duniya cikin hadari ba.

Yiwuwar bijiro da wani kudiri da zai caccaki matakin na Iran a taron majalisar zartaswar ya janyo tsokaci daga kwararru a fannin diflomasiyya gabanin taron, inda aka jiyo ministan harkokin wajen Iran din Javad Zarif  na cewa, Turawa sun dauko hanyar da ba za ta bulle ba.

A yayin da shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyar maido da kasarsa cikin yarjejeniyar ta 2015, a Lahadin nan, Iran ta ce babu dacewar shiga wata tattaunawa da Amurka da mukarrabanta, wato kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da kuma China baya ga Rasha.

Majiyoyin diflomasiyya sun ce kasashen Turai ba su cimma matsaya a  game da bijiro da wani kudiri ba, sakamakon cewa nan gaba a wannan makon ne za a tattauna batun Iran a taron da suke ta kafar bidiyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.