Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta sake dakile yunkurin mayakan Houthi na kaiwa birnin Riyadh farmaki

Rahotanni daga Saudiya sun ce an jiyo kara mai karfin gaske a sassan birnin Riyadh, wadda da rundunar sojin kasar ta ce ta wani makami mai linzami ne da ta tarwatsa, bayan da mayakan Houthi suka yi yunkurin kaiwa birnin na Riyadh farmaki.

Wani makami mai linzami da kasar Iran ta kera.
Wani makami mai linzami da kasar Iran ta kera. AP
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Saudiya tace jumillar makamai masu linzami 6 ta tarwatsa, wadanda ‘yan tawayen na Houthi suka harba daga Yemen zuwa wasu biranen kasar ta Saudiya baya ga Riyadh.

Dakile yunkurin kai farmakin da mayakan na Houthi suka yi, na zuwa ne sa’o’i bayan kazamin fadan da ‘yan tawayen suka gwabza da sojojin Yemen a birnin Ma’arib, inda akalla mayaka 50 suka rasa rayukansu daga bangarorin biyu.

Har yanzu dai mayakan na Houthi basu dauki alhakin harba makaman masu linzami kan Saudiya ba, sai dai a baya sun sha yin ikirarin kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki kan wasu yankunan kudancin kasar, baya ga yunkurin farwa birnin Riyadh a lokuta da dama.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.