Isa ga babban shafi
Yemen

Za mu dawo da doka da oda a Yemen - Gwamnati

Kwana daya bayan kazamin harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 26 a kasar Yemen, sakamakon tagwayen fashe-fashen da ake kyautata zaton bama bamai ne a filin jiragen sama na Aden,gwamnatin kasar ta dau alkawali na dawo da doka da oda

Taron sulhunta rikicin Yemen a Saudiya tareda  Mohammed ben Zayed, Mohammed ben Salman na Saudiya da Shugaban yemen a Riyad.
Taron sulhunta rikicin Yemen a Saudiya tareda Mohammed ben Zayed, Mohammed ben Salman na Saudiya da Shugaban yemen a Riyad. Saudi Press Agency/Handout via REUTERS
Talla

Jami’an agaji sun ce sama da mutane 50 suka jikkata, tare da bayyana fargabar hauhawar adadin wadanda tashin hankalin ya rutsa dasu, sai dai dukkanin jami’an gwamnatin da suka suka a filin jiragen sun tsira ba tare da raunuka ba.

A cewar Ministan harakokin wajen kasar Ahmed Ben Moubarak,gwamnati tareda hadin gwuiwar kasashen Duniya za ta dawo da doka da oda a fadin kasar Yemen, kasar da ta share shekaru ta na fama da yaki, banda haka ga talauci da yayi wa kasar kanta.

Jami'in gwamnatin kasar ya ce bincike na tafiya a kai don zakulo masu hannu a wannan kazamin hari da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26 tareda raunata da dama

Tawagar jami’an sabuwar gwamnatin ta Yemen da ta kunshi ‘yan awaren da a baya ke neman ballewar kudancin kasar, ta sauka a filin jirgin Aden ne, bayan rantsar dasu a Saudiya, ranar 18 ga watan Disamban nan mai karewa.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai farmakin, sai dai wasu daga cikin mukarraban gwamnatin Yemen da ska hada da Ministan yada labarai Mo’ammar al-Eryani da kuma Ministan harkokin waje Ahmed bin Mubarak sun zargin ‘yan tawayen Huthi, da a yanzu ke iko da mafi rinjayen arewacin kasar ta Yemen, bayan kwace birnin Sana’a tun shekarar 2014.

.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.