Isa ga babban shafi

Interpol ta wargaza gungun 'yan fashin intanet

Rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta bayyana samun nasarar wargaza gungun masu aikata muggan laifuka ta shafukan Intanet mafi hadari a duniya, wadanda suka shahara wajen kutsen satar bayanan sirri daga komfutocin hukumomi ko daidaikun mutane.

Shafukan masu damfara ta intanet
Shafukan masu damfara ta intanet ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Rundunar ‘yan sandan na duniya sashin Turai wato Europol, tace kungiyar mai suna EMOTET, ta yi fice wajen kutse ta shafukan Intanet don satar bayanan manyan hukumomi, bankuna, har da manyan asibitoci, baya ga daidaikun mutanen da ta’asar kan rutsa dasu.

Bincike dai ya nuna cewar, gungun masu kutsen na na yin dabarar aikewa da sakwannin mail da suka yi kama da na bayanan kudi, hada-hadar kasuwanci ko kuma jan hankali kan annobar coronavirus, wajen yaudarar jama’a, wanda da zarar sun bude sakwannin, bayanansu dake komfutoci za su kulle, ba kuma za su sake budewa ba, har sai an biya makudan kudaden fansa.

Rundunar ‘yan sandan ta Europol tace gungun ‘yan fashin na Intanet na yin amfani da nau’ikan manhajojin da ake kira da botnet ne wajen sarrafa komfutocin da suka kaiwa hari, ta yadda suka so.

Jami’ai ‘yan sanda daga Birtaniya, Canada, Jamus, Lithuania, Netherlands, Ukraine da kuma Amurka ne suka hada gwiwa wajen wargaza EMOTET, gungun masu aikata laifuka ta shafukan intanet mafi hadari a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.