Isa ga babban shafi
Coronavirus

Adadin masu Coronavirus ya haura miliyan 100 a sassan Duniya

Adadin mutanen da cutar Covid-19 ta harba a sassan Duniya yanzu haka ya zarce miliyan 100, yayında sama da miliyan 2 da dubu 100 saka rasa rayukan su.

Har yanzu dai Amurka ce jagora a jerin kasashen da ke da yawan masu fama da Coronavirus.
Har yanzu dai Amurka ce jagora a jerin kasashen da ke da yawan masu fama da Coronavirus. REUTERS/Alexandre Meneghini
Talla

Kasar Amurka ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka harbu da cutar, wadanda suka zarce miliyan 25, kuma sama da dubu 420 daga cikinsu sun mutu.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyar sayen karin maganin rigakafi miliyan 200 domin amfani da miliyan 300 wajen yiwa jama’ar kasar rigakafi, a daidai lokacin da yake bayyana halin da Amurka ta samu kań ta a matsayin yanayin yaki.

A bangare guda Birtaniya ta zama kasa ta farko a Turai da adadin mutanenta wadanda Covid-19 ta hallaka ya haura dubu 100 inda Firaminista Boris Johnson ke cewa lallai nauyi ne daya rataya a wuyansu bayar da kariya ga rayukan al’umma kuma ci gaba da rasa rayukan mutanen sanadiyyar cutar na taba zuciyarsu matuka.

Tuni dai kasashen Duniya suka fara sake daukar tsauraran matakan dakile cutar ta hanyar kulle jama’arsu ciki kuwa har da Brazil a kan gaba kana Afrika ta kudu dai dai lokacin da kwararru ke bayar da shawarar daukar makamancin matakin a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.