Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta kasance kasa ta farko da ta soma amfani da allurar rigakafin coronavirus

Masar ta fara yiwa yan kasar alluran rigakafin cutar Covid-19, inda ta zama kasa ta farko a Afirka da ta fara amfani rigakafin, bayan da wani likita da wata ma’aikaciyar jinya suka fara karban allurar Sinopharm da kasar China ta samar.

Maganin allurar rigakafin da China ta samar na Sinopharm
Maganin allurar rigakafin da China ta samar na Sinopharm AP Photo/Mark Schiefelbein
Talla

Masar mafiya yawan alumma a kasashen Larabawa da sama da mutane miliyan 100, ta karbi kashin farko na rigakafin da kamfanin harhada magunguna na kasar China Sinopharm ya samar ne a watan Disamba.

A cewar ministan lafiyar kasar Masar Hala Zayed, Alurar rigakafin za ta kasance kyauta ga daukacin ma ́aikatan kiwon lafiya kasar, tana mai jimamin likitocin kasar 330 da cutar ta kashe a kasar.

Mutanen da ke fama da cututtuka masu tsanani da gajiyayyu zasu bi sahun ma'aikatan kiwon lafiya wajen samun rigakafin cutar, to sai dai ministan tace sauran 'yan kasa dake da hali zasu fanshi maganin da kudinsu a watanni masu zawa.

Sama da mutane 160,000 suka harbu da cutar a kasar Masar, yayin da cutar ta kashe kimanin dubu 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.