Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun halaka 'yan ta'adda 40

Rundunar sojin Masar ta ce dakarunta sun halaka ‘yan ta’adda 40 a wani farmakin sama da suka kaddamar a  cikin watan Satumba a yankin Sinai wanda ya yi kaurin suna wajen zama matattarar masu tayar da kayar baya.

Dakarun Masar a fagen-daga a yankin Sinai
Dakarun Masar a fagen-daga a yankin Sinai REUTERS/Ministry of Defence/Handout
Talla

Cikin wani sakon bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook, rundunar sojin ta Masar ta yi amfani da kalmar ‘takfir’ wajen nuni ga ‘yan ta’addan da ta halaka a arewa maso gabashin yankin na Sinai.

Sanarwar ta kuma bayyana kame wasu ‘yan ta’addan 12 yayin da sojoji 7 ko dai suka jikkata ko kuma suka mutu yayin gurmurzu da masu tada kayar bayan.

Sojin na Masar sun ce daga watan Satumban da ya gabata zuwa yanzu, sun samu nasarar lalata nau’ukan muggan makamai 437, tare da kwance bama-bamai 159.

Tun watan Fabarairun shekarar 2018, sojojin Masar suka kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a arewacin yankin Sinai, kuma kawo yanzu sun samu nasarar kashe masu tada kayar bayan kimanin 970, yayin da suka rasa gwamman jami’ai a nasu bangaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.