Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun halaka 'yan ta'adda sama da 70 a arewacin Sinai

Rundunar sojin Masar bayyana samun nasarar halaka mayakan ‘yan ta’adda sama da 70, yayin farmakin baya bayan nan da ta kaddamar kan su a Arewacin Sinai, yankin bayanai suka ce tsirarun mayakan kungiyar IS ke kokarin amfani da shi wajen sake kafuwa.

Wasu sojojin kasar Masar.
Wasu sojojin kasar Masar. AFP
Talla

Sanarwar rundunar sojin Masar din tace ta kaddamar da farmakin ne a tsakanin 22 ga watan Yuli zuwa 30 ga watan Agusta, kuma yayin gumurzun akalla dakarunsu bakwai ne ko dai suka jikkata, ko kuma suka rasa rayukansu.

Cikin watan Fabarairu na shekarar 2018, sojojin masar suka kaddamar da yaki kan ‘yan ta’adda a sassan kasar, musamman a Arewacin Sinai.

Rahoton baya bayan nan yace tun bayan kaddamar da farmakin a 2018, dakarun na Masar sun halaka mayakan ‘yan ta’adda sama da 930, yayinda gwamman jami’an tsaro suka rasa rayukansu yayin fafatawar.

Har yanzu dai babu wata kungiya ko kafar yada labarai mai zaman kanta da ta tabbatar da alkaluman ko rahoton da rundunar sojin Masar din ke fitarwa, sakamakon haramtawa ‘yan jaridu da kungiyoyin fararen hula ziyartar yankin na Arewacin Sinai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.