Isa ga babban shafi
Coronavirus

Kamfanoni 48 na rige-rigen samar da maganin Korona- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa akwai kamfanonin magunguna 48 da yanzu haka ke rige-rigen samar da maganin cutar coronavirus wadanda kuma rabinsu ke gab da kammala fitar da maganin ga jama’a.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO.
Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO. 路透社图片
Talla

A cewar hukumar ta WHO daga kamfanoni 11 a tsakiyar Yunin da ya gabata, yanzu haka akwai kamfanoni 48 wadanda aka aminta da ingancinsu da ke aikin samar da maganin na coronavirus wadda zuwa yanzu ta kashe mutane miliyan 1 da dubu dari 4 a sassan Duniya tun bayan bullarta a tsakiyar watan Disamban bara.

Bayanan hukumar na nuna cewa ana samun gagarumin ci gaba a kokarin kamfanonin na samar da maganin cikin gaggawa inda yanzu haka kamfanoni 11 ke mataki na 3 wajen samar da maganin kuma tuni suka yi gwajin na su nau’ikan magungunan a jikin bil’adama ba kuma tare da an samu wata matsala ba.

A nahiyar Turai kamfanin AstraZeneca da hadin gwiwar jami’ar Oxford da ke aikin hadin gwiwa wajen samar da maganin na corona wanda shi ma ke mataki na 3 sun sanar da sake samun kwarin gwiwa bayan nasarar maganin da akalla kashi 70 cikin dari kan mutane dubu 23 da aka yiwa gwajinsa.

Hadakar kamfanin na AstraZeneca da Jami’ar Oxford sun sanar da cewa maganin na da wa’adin akalla watanni 6 gabanin ya lalace kuma za a iya tafiya mai nisa da shi amma a cikin firji ko kuma na'urar sanyaya magunguna, wanda ke nuna cewa nan da shekarar 2021 za su samar da maganin kimanin miliyan 3 baya ga sake kyautata shi.

A bangare guda hadakar kamfanonin magani na Amurka da Jamus wato BioNTech da Pfizer sun tabbatar da sahihancin maganinsu na mRNA wajen warkar da mutane da aka yiwa gwajinsa da akalla kashi 95.

Sanarwar kamfanin ta nuna cewa nau’in maganin ya warkar da mutane a mabanbantan shekaru da jinsi har ma da launin fata, wanda ke nuna za a iya amfani da shi kan kowanne nau’in mutane.

Haka zalika a China kadai akwai tarin dakunan gwaji da ke ci gaba da aikin samar da maganin cutar yayinda Rasha tuni ta fara amfani da biyu daga cikin nata nau’ikan magungunan da ta samar tun ma gabanin a kammala tabbatar da sahihancinsa a dakunan gwaji kuma ya ke ci gaba da warkar da jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.