Isa ga babban shafi
Amurka

Amurkawa Miliyan 17 sun kada kuri'unsu gabanin ranar zaben watan gobe

Yayinda ya rage kasa da makwanni 3 a gudanar da zaben shugaban Amurka, kaso mai yawa na al’ummar kasar da yawansu ya haura miliyan 17 tuni sun kada kuri'unsu adadin da ke matsayin mafi yawa da aka taba gani a tarihi na yawan mutanen da suka kada kuri’ar da wuri yayin zaben na watan Nuwamba da za a kara tsakanin shugaba Donald Trump na Jam’iyyar Republican da Joe Biden na Jam’iyyar Democrat.

'Yan takarar shugabancin Amurka a zaben watan Nuwamba shugaba Donald Trump na Republican da tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden na Jam'iyyar Demokrat.
'Yan takarar shugabancin Amurka a zaben watan Nuwamba shugaba Donald Trump na Republican da tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden na Jam'iyyar Demokrat. AP/Patrick Semansky
Talla

Rahotanni sun ce, yayin da sai ranar 3 ga watan Nuwanba bayan zaben gama gari za’a san wanda ya samu nasara, majiyoyi da dama na nuna cerwar Joe Biden yafi samun kuri’u daga cikin wadanda aka riga aka kada.

Daga cikin jihohin da aka bai wa damar kada kuri’u da wuri har da Jihar Iowa inda shugaba Donald Trump ya gudanar da yakin neman zabe ranar laraba, kuma ya zuwa yau alhamis mutane sama da 325,000 suka riga sun kada kuri’un su kamar yadda Jami’ar Florida da ke sanya ido akan yadda zaben ke gudana ta sanar.

Jami’ar ta ce ya zuwa safiyar Alhamis din nan mutane miliyan 17 da dubu 360 sun kada kuri’un su a Jihohin da aka fara gudanar da zaben wanda aka danganta fitowar mutane da yunkurin kaucewa kamuwa da cutar korona.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a ya nuna cewar magoya bayan Jam’iyyar Democrat da dama sun gwammace kada kuri’a da wuri kafin ranar zabe a maimakon 'yan Republican, yayin da shugaba Donald Trump ke cigaba da bayyana adawar sa da masu aikewa da kuri’un su ta gidan waya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.