Isa ga babban shafi
Amurka

Mujallar Nature ta goyi bayan Biden a zaben Amurka na watan gobe

Yayin da lokacin zaben shugaban kasar Amurka ke kara karatowa, Mujallar Nature ta bayyana goyan bayan ta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden wajen ganin ya samu nasarar lashe zaben akan shugaba Donald Trump mai-ci saboda abinda ta kira irin illar da ya yiwa Amurka wajen tinkarar annobar korona wadda ta kashe mutane sama da 215,000 a cikin kasar.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar Democrat Joe Biden.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar Democrat Joe Biden. AP Photo/Patrick Semansky
Talla

Mujallar wadda ke cikin fitattun kafofin yada labaran da ke mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi muhalli da kuma ake ganin kimar su a duniya, ta ce a tarihin Amurka, ba a taba samun shugaban da ke zagon kasa ga hukumomin kimiya da na shari’a da kuma zabe irin Donald Trump ba.

Mujallar ta cacaki shugaba Trump kan yadda ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar sauyin yanayin da aka kulla a Paris ta 2015 da yarjejeniyar nukiliyar Iran da kuma irin yadda ya ke kai wa hukumar lafiya ta Duniya hari, abinda ta bayyana a matsayin abinda hankali ba zai dauka ba lokacin da ake fama da annoba.

Nature ta ce yadda shugaba Trump ke bijirewa dokoki da gwamnatoci da kimiya da hukumomin dimokiradiya duk da ganin shaidu karara sun nuna cewar bashi da kimar jagorancin Amurka.

Babban Editan Mujallar Magdelena Skipper ta ce Trump ya rasa kimar sake zama shugaban Amurka saboda haka suna goyan bayan Joe Biden wanda ya yi alkawarin mayar da kasar cikin yarjejeniyar Paris da kuma amfani da shawarwarin masana kimiya wajen tinkarar annobar korona da kuma sauya matakai da dama da Trump ya dauka wadanda suka yiwa Amurka illa.

Kafin dai Mujallar Nature, Jaridar Washington Post ta bayyana goyan bayan ta ga takarar Joe Biden, yayin da Mujallar kula da lafiya ta ‘The New England Medical Journal’ ta cacaki gazawar shugaba Trump wajen kare lafiyar Amurkawan da suka mutu sakamakon korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.