Isa ga babban shafi
Zaben - Amurka

Harris da Pence sun fafata muhawarar neman mataimakin shugabancin Amurka

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence yace babu abinda zai hana shugaba Donald Trump samun nasara a zaben shugaban kasar da za’ayi a watan gobe, saboda gagarumar nasarar da suka samu wajen dawo da martabar Amurka.

'Yan takarar mataimakan kujerar shugabancin Amurka Mike Pence da Kamala Harris, yayin muhawara da suka gudanar
'Yan takarar mataimakan kujerar shugabancin Amurka Mike Pence da Kamala Harris, yayin muhawara da suka gudanar Justin Sullivan/Pool via AP/ Fotomontagem RFI
Talla

Yayin mahawara ta farko tsakanin sa da Kamala Harris, wadda zata marawa Joe Biden baya a zabe mai zuwa, Pence yace Amurkawan da suka zabi Trump a shekarar 2016 su zasu sake zaben sa saboda gamsuwa da rawar da ya taka.

Mike PENCE

"Susan da farko zan fada miki cewar mu zamu lashe wannan zabe. Shugaba Donald Trump yana kaddamar da wata tafiya kowacce rana, Amurkawa na samun aiki, kuma ina da yakinin cewar Amurkawar da suka kafa tarihin zaben shi a shekarar 2016, kuma sun ga irin nasarorin da ya samu. Mun sake gina sojojin mu, ta hanyar zabtare haraji da sauya wasu dokoki, da yaki domin tabbatar da daidaito a bangaren kasuwanci, da gabatar da makamashin da Amurka ke da shi. Mun cika kotunan mu da ‘yan ra’ayin rikau a kowanne mataki, kuma mun jajirce wajen goyan bayan jami’an tsaron mu kowacce rana. Ina ganin zamu lashe wannan zabe. Shugaba Trump da ni na yaki kowacce rana a kotuna domin hana Joe Biden da Kamala Harris sauya dokoki wajen sanya kada kuri’u ta gidan waya, wanda zai bada damar tafka magudi. Idan an samu zabe sahihi, mun sani zamu goyi bayan sa, kuma ina da yakini a cikin zuciya ta, za’a sake zaben shugaba Donald Trump na Karin shekaru 4".

Itakuwa 'Yar takarar kujerar mataimakin shugaban Amurka a Jam’iyyar Democrat, Kamala Harris ta bayyana jagorancin shugaba Donald Trump wajen magance cutar korona a kasar a matsayin mummunar koma bayan da zata haramta masa samun wa’adi na biyu.

Harris tace Amurkawa sun gani da idan su mummunar gazawar da wannan gwamnatin tayi wanda ba’a taba gani ba a tarihin Amurka, inda tace wannan kawai ya isa a raba shi da karagar mulki.

Sai kuma ta bukaci Amurkawa da suyi tururuwa wajen kada kuri’u.

Kamala HARRIS

"Mun amince da mutanen Amurka, mun amince da dimokiradiyar mu, ga abinda zan shaidawa kowa, ku kada kuri’a. dan Allah ku kada kuri’a, kuma kuyi da sauri. Ku samo dabarar kada kuri’a, wajen zuwa ‘ill vote.com’, kuma kuna iya kada kuri’a ta ‘joebiden.com’. muna da iko a cikin wadannan kwanaki 27 mu yanke hukunci akan abinda zai faru wajen tafiyar da kasar mu a cikin shekaru 4 masu zuwa. Kuma yana karkashin ikon mu ne. kuma idan mun yi amfani da kuri’ar mu, idan mun yi amfani da muryar mu, zamu samu nasara. Kuma ba zamu bari wani ya yiwa dimokiradiyar mu zagon kasa ba, kamar yadda Donald Trump ke cigaba da yi, kamar yadda yayi ranar mahawarar da akayi makon jiya, a gaban mutane miliyan 70, ya nuna kararara yadda yake kokarin watsi da sakamakon zaben".

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.