Isa ga babban shafi
Amurka

Biden ya zabi Kamala Harris a matsayin wadda zata mara masa baya

Dan takarar Jam’iyyar Democrat a zaben Amurka Joe Biden ya zabi Sanata Kamal Harris a matsayin wadda zata mara masa baya, inda ta zama mace bakar fata ta farko da zata rike wannan mukami idan sun samu nasara.

Joe Biden  da Sanata Kamala Harris, a lokacin fidda gwani a zaben Democrats na Amurka
Joe Biden da Sanata Kamala Harris, a lokacin fidda gwani a zaben Democrats na Amurka REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Sanar da sunan Sanata Kamala Harris ya kawo karshen watannin da aka kwashe Jam’iyyar Democrat na lalubo wanda zai marawa Joe Biden baya domin kawar da shugaba Donald Trump daga shugabancin Amurka a zaben watan Nuwamba.

Biden ya bayyana Harris a matsayin mara tsoro da kuma daya daga cikin ingantattun ma’aikatan da suka yiwa Amurka aiki, inda yake cewa cike yake da farin ciki wajen zabo ta,don  ta mara masa baya.

Ana saran Sanata Harris mai shekaru 55 ta janyo ra’ayin matasa, mata da kuma bakaken fata wajen samun nasarar zaben mai zuwa.

Tuni zabin nata ya gamu da martani daga sassa daban daban na Amurka, ciki harda tsohon shugaban kasa Barack Obama da Sanata Hillary Clinton wadanda suka yaba da zabin, yayin da shugaba Donald Trump ya soke ta a matsayin wadda ta kasa katabus lokacin da ta tsaya takarar fidda gwani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.