Isa ga babban shafi

Kashi 10 na al'ummar duniya sun kamu da coronavirus - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kiyasta cewa kashi 10 cikin 100 na al’ummar duniya ne suka harbu da annobar corobnavirus, adadin da ya zarta alkalumar da aka bayar a bayan.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Sama da mutane miliyan 35 aka tabbatar sun harbu da cutar korona a fadin duniya, yayin da wasu sama da miliyan 1 da dubu 400 suka mutu, Kafin wannan sabon rahoton na Hukumar Lafiyar ta Duniya.

To sai dai a yanzu WHO na kiyasin cewa kusan kashi goma na al’ummar duniya biliyan biliyan 7 da miliyan 800 ne suka kamu da cutar tun bayan bullarta bara a kasar China.

Darektan gaggawa na Hukumar Lafiyar ta Duniya, Michael Ryan da ya bayyana hakan yayin taron gaggawa na kwamitin zartarwar hukumar, yace har yanzu duniya na cikin barazanar annobar covid -19.

Ko daya yake tuni wasu kasashe suka farga wajen sake fasalta matakan kariya daga yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.