Isa ga babban shafi

Trump da Baiden sun soki juna a muharawarsu ta farko

'Yan Takarar shugabancin Amurka a zaben da zai gudana ranar 3 ga watan Nuwamba, shugaba Donald Trump na Republican da abokin karawar sa Joe Biden na Democrat sun tafka mahawara ta farko cikin muhawarori uku dangane da shirin zaben, inda suka yi ta sukar manufofin juna.

'Yan takarar neman shugabancin Amurka Donald Trump da Joe Biden yayin muhararsu ta farko
'Yan takarar neman shugabancin Amurka Donald Trump da Joe Biden yayin muhararsu ta farko REUTERS/Brian Snyder
Talla

Wannan muhawara mai zafi ya kunshi tambayoyi 6-6 cikin batutuwa shida dan jarida ya jagoranci muhuwar yayiwa bangarorin 'yan takararar biyu, inda aka basu minti 15 domin amsa tambayoyin da mayar da martani.

Batutuwan da suka hada da tattalin arziki da cutar korona da ta kashe mutane sama da 200,000 a kasar da rarrabuwar kawuna tsakanin farare da bakake da batun sauyin yanayi da tashe tashen hankula ne suka mamaye mahawarar.

Saboda cutar korona mutane kalilan aka bari suka halarci zaman muhawarar, ciki har da iyalan 'yan takarar na kusa da su, Maidakin Mista Trump Melania da kuma na Joe Biden JIll sun harci muhawarar.

To sai dai tun kafin a je ko'ina, 'yan takarar biyu suka fara caccakar-manufofin juna, inda suka kaure da bakaken maganganu da zage-zagen juna.

An dai bude muhawarce da butun nada sabuwar alkalin kotun kolin Amurka da za ta maye gurbin wadda ta mutu cikin yanayin daf da zaben na 2020.

Donald Trump dai ya bayyana cewa yanzu ya kamata a zabi sabuwar shugar kotun, yayin da Joe Biden ke cewa ya kamata a bar Amurkawa su bayyana ra'ayinsu akai.

A karshe, shugaba Trump ya sake bayyana shakkun sa kan sahihancin zaben da za’ayi, inda yake cewa idan bai gamsu ba, ba zai amince da sakamakon sa ba, inda ya kira magobayansa da suka kasa su tsare, sabanin Biden wanda ya nuna kwarin gwuiwar sa akan shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.