Isa ga babban shafi
Amurka

Democrat ta soma babban taron kaddamar da dan takararta a zaben Amurka

An bude babban taron Democrat domin kaddamar da dan takarar jam’iyyar a zaben shugabancin kasar Amurka da za a yi cikin watan nuwamba Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris.

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrats Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrats Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris Robyn Beck / AFP
Talla

Za a shafe akalla kwanaki 4 ana gudanar da taron amma ta hoton bidiyo saboda annobar coronavirus.

Daga cikin wadanda aka tsara za su gabatar da jawabai ga taron, sun hada da dan takarar da mataimakiyarsa, sai kuma fitattun ‘yayan jam’iyyar da suka hada da tsohon shugaba Barack Obama da matarsa Michelle, sai kuma tsohon shugaba Bill Ciliton da matarsa Hillary.

Har ila yau ana dakon jawabai daga ‘yan takarar Democrat da suka sha kaye a zaben fidda gwani irinsu Elizabeth Warren, yayin da tuni Bernie Sanders ya gabatar da nasa jawabi da a ciki yake jaddada goyon bayan ganin an kawar da Donald Trump daga karagar mulki a zabe mai zuwa.

01:00

Sanata Bernie Sanders kan alwashin kawar da shugabancin Donald Trump

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.