Facebook da Twitter sun dauki mataki kan Trump
Kamfanonin sadarwa na Facebook da Twitter sun dauki mataki kan shugaban Amurka Donald Trump bisa wani hoton bidiyo da aka wallafa, inda a cikinsa shugaban ke ikirarin cewa, kananan yara na da garkuwar hana kamuwa da cutar coronavirus.
Wallafawa ranar:
Kamfanin Facebook ya goge hoton bidiyon wanda aka yanko daga cikin wata hira da shugaban ya yi da kafar Fox News, yayin da kamfanin ke cewa, bidiyon na dauke da bayanan karya masu cutarwa.
Shi kuwa Twitter cewa ya yi, ya dakatar da dandalin yakin neman zaben shugaba Trump a shafin har sai an janye hoton bidiyon.
Shawarar da Hukumar Kula da Lafiyar Al’umma ta Amurka ta bayar ta nuna cewa, kananan yara ba su da wata kariyar hana kamuwa da cutar Covid-19.
A karon farko kenan da Facebook ke daukar matakin janye sakon da shugaba Trump ke wallafawa bayan Kamfanin ya ce sakon ya saba da dokokinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu