Isa ga babban shafi

Zan iya shan kaye a zabe mai zuwa - Trump

Ga alama shugaban Amurka Donald Trump ya ji a jikin sa cewar ba zai samu nasarar zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Nuwamba ba, sakamakon yadda sau biyu a wannan mako yana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai kada shi a zabe mai zuwa.

Shugaban Amurka Donald Trump, yayin gangamin siyasa a Tusla na kasar , ranar  20 ga watan  2020.
Shugaban Amurka Donald Trump, yayin gangamin siyasa a Tusla na kasar , ranar 20 ga watan 2020. REUTERS/Leah Millis
Talla

A wata hira da yayi da Sean Hannity ta tashar Fox News, shugaba Donald Trump ya nuna alamun bada kai bori ya hau, inda yake cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai kada shi a zaben watan Nuwamba mai zuwa.

A hirar Trump yace Biden zai samu nasarar ce saboda wasu mutane basa son sa a Amurka, kuma wannan shi zai baiwa tsohon mataimakin shugaban nasara.

Kafin wannan hirar, shugaba Trump ya shaidawa magoya bayan sa taron da ya gudanar a Winsconsin, cewar Biden ya tsufa da ba zai iya shugabanci ba, domin yana fama da matsalar gane mutane. Shugaban ya kara da cewar Biden baya iya iyin kalamai guda biyu a jere, kuma baya iya Magana.

Daga nan Trump yace Biden zai zama shugaban kasa ne kawai saboda wasu Amurkawa basa son sa, kuma shi babu abinda yake sai gudanar da ayyukan sa kamar yadda doka ta tanada.

Dangane da gina Katanga tsakanin Amurka da Mexico kuwa, shugaba Trump yace idan Biden ya samu nasara zai karasa aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.