Isa ga babban shafi
Amurka

Zaben Amurka: Biden na gaf da samun tikitin fafatawa da Trump

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya samu nasara a zaben fidda dan takara da jam’iyyar Democrat ta gudanar cikin jihohi uku a ranar talata, lamarin da ke kara share masa fage a yunkurinsa na samun damar tsayawa jam’iyyar a zaben shugabancin kasar na watan nuwamba mai zuwa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden dake neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Democrats.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden dake neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Democrats. REUTERS/Carlos Barria
Talla

An gudanar da zaben na jiya talata ne a johohin Florida, Illinois da kuma Arizona, kuma sakamakon farko na nuni da cewa Joe Biden ya baiwa abokin hamayyarsa Bernie Sanders tazara a jihohin uku.

Duk da cewa an gudanar da zaben ne a cikin yanayi na fargaba sakamakon annobar Coronavirus da kuma janyewar sauran ‘yan takara daga zaben, an samu fitowar masu kada kuri’a.

A jihar Florida, tsohon mataimakin shugaban kasar Biden mai shekaru 77 a duniya ya lashe zaben da 62% inda Bernie Sanders ya samu 23%. A can ma jihar Illinois Biden ya bai wa Sanders tazarar maki 23, yayin da Arizona inda aka kammala zaben a makare Biden ya sake yin nasara kamar dai yadda alkaluma suka nuna.

Wannan dai na tabbatar da cewa Joe Biden ya samu galaba har sau 19 daga fafatawa 24 da ya yi da sauran ‘yan takara a sassan kasar ta Amurka, abin da ke kara share masa fage domin karawa da shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican a zaben na watan nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.