Isa ga babban shafi
Duniya

Coronavirus na barazanar raba mutane biliyan 1.6 da sana’o’insu

Kungiyar Kwadago ta Duniya wato International Labour Organisation ILO, ta ce kusan rabin hanyoyin da mutanen duniya suka dogara da su don samun abinci, za su ruguje baki daya sakamakon annobar COVID-19.

Wasu masu sana'ar saida kayayyaki a birnin Lahore na Pakistan a dai dai lokacin da dokar hana fita ke aiki saboda coronavirus. 14/4/2020.
Wasu masu sana'ar saida kayayyaki a birnin Lahore na Pakistan a dai dai lokacin da dokar hana fita ke aiki saboda coronavirus. 14/4/2020. Arif Ali/AFP
Talla

Sanarwar da kungiyar ta ILO ta fitar, ta ce matsalar za ta fi shafar mutanen da suka dogara da kananan sana'o'i ne da yawansu za su kai biliyan daya da milyan 600 a sassan duniya.

Kungiyar kwadagon ta yi gargadin cewa kafin karshen watanni 6 na farkon wannan shekara ta 2020 ne wadannan mutane za su fada cikin matsalolin da Coronavirus ta haifar wa bangaren ayyukan kwadago da sauran abubuwan da jama'a suka dogara dasu domin rayuwa.

Guy Ryder, daraktan kungiyar ta ILO, ya ce yanzu haka a duniya baki daya akwai mutane bilyan uku da wasu milyan 300 dake fita kowace rana ta Allah domin aiki ko sana'a, to amma rabinsu ko dai suna zaman kashe wando ko kuma harkokinsu sun tsaya cik sakamakon wannan annobar.

ILO ta bayyana wasu daga cikin fannonin da suka fi fama da radadin cutar ta coronavirus, da suka hada da bangaren gine-gine, wuraren sayar da abinci, manyan kamfanoni da masana'antu da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.