Isa ga babban shafi
Coronavirus

British Airways zai sallami ma'aikatansa dubu 12

Katafaren kamfanin sufurin jiragen sama na British Airways, ya bayyana shirin sallamar ma’aikatansa dubu 12, a karkashin wani shirin gudanar da sauye-sauye a dalilin illar da cutar coronavirus ta yiwa harkokinsa.

Wasu jiragen saman kamfanin British Airways a filin jiragen sama na Heathrow dake arewacin birnin London a Birtaniya. 23/2/2018.
Wasu jiragen saman kamfanin British Airways a filin jiragen sama na Heathrow dake arewacin birnin London a Birtaniya. 23/2/2018. REUTERS/Hannah McKay/File Photo
Talla

Kamfanin IAG da ya mallaki kamfanin na ritish Airways yace yana cigaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan shirin daukar matakin, amma ya bada tabbacin cewar tabbas zai sallami dubban ma’akatan nasa.

Kamfanin yace za a dauki shekaru da dama kafin ya koma gudanar da harkokinsa kamar yadda ya saba bayan shawo kan annobar coronavirus da ta kashe mutane sama da mutane dubu 214 a fadin duniya.

British Airways na da matuka jirage dubu 4 da 500 da masu aiki a cikin jirage dubu 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.