Isa ga babban shafi
Coronavirus

'Shekaru 100 raban da arzikin duniya ya durkushe'

Shugabar Asusun Bada Lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva, ta ce annobar coronavirus na ci gaba da kassara tattalin arzikin duniya cikin yanayi mafi muni da aka taba gani fiye da shekaru 100 da suka gabata. 

Kristalina Georgieva shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF.
Kristalina Georgieva shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Shugabar Asusun na IMF ta yi gargadin cewa, tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya kai tsaye a wannan shekara ta 2020, la’akari da cewar tattalin arzikin kasashe 170 daga cikin 180 da ke bin tsare-tsaren asusun bada lamunin na duniya ya durkushe biyo bayan tasirin annobar coronavirus.

Asusun na IMF ya bayyana fatan farfadowar tattalin arzikin duniya ne a shekara mai kamawa idan aka yi sa’ar kawo karshen annobar murar ta COVID-19 cikin wannan shekara, abin da zai bada damar ci gaba da ayyukan masana’antu, da harkokin kasuwancin da annobar ta tilasta dakatar da su, biyo bayan killace kusan rabin al’ummar duniya da hukumomi suka yi don dakile cutar.

Kididdgar masana ta nuna cewar, kawo yanzu a jimlace gwamnatocin kasashe sun dauki matakan da suka lakume akalla Dala tiriliyan 8 don yakar annobar coronavirus, sai dai akwai bukatar kari, a cewar Kristalina.

Georgieva ta ce, yanzu haka kasuwannin duniya sun tafka asarar kimanin Dala biliyan 100 a dalilin kauracewar masu zuba hannun jari, duk dai saboda tasirin annobar COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.