Isa ga babban shafi
China-Corona

Coronavirus ta kashe mutane sama da 1000 a China

Shugaban kasar China Xi Jinping ya sha alwashin kawo karshen cutar coronavirus dake cigaba da yaduwa kamar wutar daji, bayan ta kama mutane sama da dubu 42,600 da kuma hallaka sama da 1000 yanzu haka.

Xi Jinping shugaban kasar China a yayinda ya ziyarci wani asibiti a Beijing
Xi Jinping shugaban kasar China a yayinda ya ziyarci wani asibiti a Beijing (Foto: AFP/XINHUA / JU Peng)
Talla

Sanye da tsummar dake rufe fuska, shugaban kasar China Xi Jinping ya gwada zafin jinkin sa lokacin da ya ziyarci asibitin dake kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus wanda ta kasha mutane 1,011.

Yayin ziyarar shugaba Xi ya bayyana cutar a matsayin abu mai girma dake bukatar kwararan matakai domin hana yaduwar ta.

Shugaban ya gana da likitoci da kuma marasa lafiyar dake asibitin Ditan dake Beijing, yayin da ya kalli yadda ake kula da su a Wuhan ta bidiyo.

Daga bisani shugaban ya ziyarci tsakiyar birnin Beijing domin sanya ido da kuma ganewa idan sa halin da ake ciki.

Wannan annoba ta sanya gwamnatin China daukar kwararan matakan da suka hada da killace miliyoyin mutane a gidajen su da katse sufurin jiragen sama da kasa da kuma rufe wuraren yawon bude ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.