Isa ga babban shafi
China-Corona

Likitan China da ya bayyana cutar coronavirus ya mutu

Wani likita dan kasar China da aka muzgunawa bayan ya fito fili ya shaida bayyana cutar masahako ta Corornavirus ya mutu a yau Juma’a, lamarin da ya tayar da hankali tare da harzuka al’umma kan cutar da ta kashe sama da mutane 630 kuma ta ke ci gaba da yaduwa.

Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya dake yaki da zazzabi a China
Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya dake yaki da zazzabi a China China Daily via REUTERS
Talla

Akalla mutane dubu 31 sun harbu da wannan cuta da likitan ido Li Wenliang da abokansa suka gano a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Cutar ta yadu a China har ma ta tilasta wa gwamnati rufe wasu birane na milyoyin mutane, yayin da aka shiga fargaba a Duniya ganin yadda cutar ta kama mutane sama da 240 a fiye da kasashe 20 a fadin Duniya.

Amurka ta bayyana fatan taimakawa China a fanin bincike,tayin da China ta yi watsi da shi a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.