Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka ta laftawa Iran sabbin takunkumai

Amurka ta hannun Sakataren baitulmalinta Steve Mnuchin ta sanar da laftawa Iran sabbin takunkuman karya tattalin arziki.

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani. © REUTERS/Brendan Mcdermid
Talla

Mnuchin ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a fadar White House dake Washington.

Sabbin takunkuman kuntatawar dai sun shafi manyan jami’an gwamnatin Iran guda 8, da kuma manyan kamfanonin dake kan gaba wajen sarrafa karafa da dangoginsa a kasar ta Iran.

Daga cikin manyan jami’an na Iran da takunkuman suka shafa akwai Ali Shamkhani babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar, da Mohammad Reza Ashtiani, mataimakin babban hafsan sojin Iran, sai kuma Gholamreza Soleimani, shugaban rundunar sojin sa kai ta Basij dake yiwa kasar ta Iran biyayya.

A bangaren kamfanonin hako ma’adanai da sarrafa karafan kasarta Iran kuwa, sabbin takunkuman na Amurka sun shafi manyan kamfanonin 17, wadanda suka saba samawa kasar kudaden shiga na biliyoyin daloli.

Amurka ta ce ta laftawa Iran sabbin takunkuman ne saboda farmakin makamai masu linzami da ta kaiwa dakarunta a Iraqi, a matsayin ramuwar kashe Qaseem Soleimani a birnin Bagadaza, daya daga cikin manyan kwamdojinta na rundunar juyin juya hali ta Quds.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.