Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sassauta kalamansa bayan harin Iran kan Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabi na farko kan farmakin ramuwar gayya da Iran ta kai wa dakarun Amurkan a Iraqi bayan kashe mata babban kwamandanta Qassem Soleimani a birnin Bagadaza. Sai dai yayin jawabin, shugaba Trump bai yi amfani da kausassan kalamai wajen raddi kan kasar ta Iran ba kamar yadda aka za ta da fari.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Wasu daga cikin batutuwan da jawabin na shugaba Trump ya tabo sun hada da gayyatar rundunar kawancen tsaro ta NATO da ta mara wa Amurka baya wajen murkushe duk wata barazana a yankin Gabas ta Tsakiya, sai kuma kira ga kasashen da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran, wato China da Jamus da Faransa da Birtaniya da Rasha da su bi sawunsa wajen ficewa daga cikin yarjejeniyar.

Shugaban ya kuma ce, Amurka za ta lafta wa Iran karin takunkuman karayar tattalin arziki har zuwa lokacin da Iran za ta sauya dabi'unta a cewarsa.

Shugaban na Amurka ya bukaci zaman lafiya a yayin wannan jawabi nasa, amma ya nanata cewa, ba zai bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojin juyin juya hali na Iran sun yi luguden wuta kan sansanonin Amurka biyu da ke Iraki a matsayin matakin farko na daukar fansar kisan Janar Soleimani.

A bangare guda, Shugabar Majalisar wakilan Amurka wadda magoya bayan Jam’iyyar Democrats ke da rinjaye Nancy Pelosi ta ce, za su kada kuri’ar hana Trump yin amfani da karfin ikonsa don kaddamar da yaki a kan Iran.

Bayan sun saurari jawabin da Trump ya gabatar, ‘yan jam’iyyar ta Democrat sun ce, shugaban bai gabatar da wasu dalilai da za su kawar da shakku dangane da illar shiga yakin ba, kuma sun bai wa sakataren harkokin waje Mike Pompeo sakon cewa, za su kada kuri’ar hana shi yin gaban kansa.

To sai dai shugaban Majalisar Dattawa wadda magoya bayan Republican ke da rinjaye Rand Paul ya ce, sun gamsu da abubuwan da ke kunshe a jawabin shugaba Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.